KRM Hausa, kafar yada labarai ce da aka kafa domin kawo wa al’umma ingantattun labarai da bayanai cikin harshen Hausa. Muna mayar da hankali wajen kawo sahihan rahotanni daga ciki Najeriya da waje, domin fadakarwa, ilmantarwa, nishadantarwa, da kuma bayyana abubuwan da ke faruwa a duniya cikin harshen Hausa.
Mun kware wajen bayar da labarai a fannoni daban-daban kamar:
Ilimi: Rahotanni da labarai masu alaƙa da cigaban ilimi a Najeriya da kasashen waje.
Wasanni: Sabbin labarai da sakamakon wasanni na gida da na duniya.
Siyasa: Bayani game da harkokin siyasa na cikin gida da na ƙasashen waje.
Nishadi: Labarai kan fina-finai, mawaka, da abubuwan nishadi masu kayatarwa.
Rayuwa da Al’adu: Rahotanni da labarai game da al’adunmu da yadda rayuwa ke gudana.
A KRM Hausa, muna aiki ne bisa doka da ƙa’idoji na aikin jarida, muna tabbatar da cewa duk wani labari da muka wallafa ya fito ne daga sahihin tushe tare da tabbatar da gaskiya da amintacciyar hanya.
Manufarmu ita ce kawo ingantattun labarai cikin Hausa, domin bunƙasa ilimi da wayar da kai ga al’umma ta hanyar harshe da suke jin daɗin fahimta.
Ku kasance tare da mu a wannan shafi domin samun sahihan labarai masu ɗumi-ɗuminsu a kowane lokaci.