An Bukaci a Tallafawa Marayu da Gajiyayyu Don Samar da Rayuwa Mai Dorewa a Gandun Albasa

Kungiyar tallafawa marayu da gajiyayyu ta Gandun Albasa, ta jaddada bukatar da ke akwai na ci gaba da tallafawa marayu da gajiyayyu domin su ma su samu rayuwa mai inganci da dorewa, musamman a cikin al'ummomin da ke fama da matsin tattalin arziki. Wannan kira ya biyo bayan taron walima da kungiyar ta shirya domin marayun da ke zaune a unguwar.



Dagacin Gandun Albasa, Injiniya Alkasim Yakubu, wanda shima ya halarci walimar, ya yaba da namijin ƙoƙarin da kungiyar ke yi wajen tallafawa marayu da gajiyayyu, musamman a fannin ilimi da tarbiyya.
Ya kara da cewa "Kungiyar na taka rawar gani, musamman wajen karfafa gwiwar marayu su ci gaba da karatu da kuma kasancewa masu amfani a al'umma. Wannan abin a yaba ne kuma muna maraba da karin goyon bayan jama'a wajen ciyar da wannan yunƙuri gaba."

Shima Shugaban Sashen Ilimi na kungiyar, Malam Nura Garba Mato, ya bayyana cewa tun daga kafuwar kungiyar zuwa yanzu, ta samu gagarumar nasara, ciki har da mayar da yara makaranta, samar da kayan karatu da kuma horas da su sana’o’i.
Mato, ya ce "Tun kafuwar kungiyar, mun mayar da yara sama da 100 makaranta, wasu kuma mun koya musu sana’o’i da suka fara dogaro da kai. Wannan al’umma tana bukatar irin wannan hadin kan da sadaukarwa."


Wasu daga cikin marayun da suka amfana da shirye-shiryen kungiyar sun bayyana farin cikinsu da irin kulawar da suke samu. Sun ce kungiyar ta ba su damar komawa makaranta, sannan ta tallafa musu da kayan abinci, tufafi da kulawa da  lafiyarsu.

An kuma yi kira ga masu hannu da shuni, hukumomi, da al’umma baki ɗaya da su mara wa kungiyar baya domin fadada ayyukanta a sauran unguwanni da yankuna.

Previous Post Next Post