Daga - Ado Danladi Farin Gida a Kano
Wasu daliban makarantun sakandaren harshen Larabci a Jihar Kano sun roki Gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf, da ya cika alkawarin da ya dauka na tura su zuwa kasashen waje domin karatu a fannin harshen Larabci.
Yayin da suke zantawa da wakilinmu, Daliban sun bayyana cewa tun bayan tantance su a matakai daban-daban – daga makarantu har zuwa matakin kananan hukumomi – inda aka tabbatar da cancantar su. Sun ce an sha yi musu alwashin za su tafi Jami’ar kasar Masar, amma har yanzu shekara guda kenan ba tare da wani cigaba ba.
Da muka tuntubi Ko’odineta na Qur’anic and Islamic Education a Ma'aikatar Ilimi ta Jihar Kano, Dr Abdulkadir Sani Aliyu Kurawa, domin jin ta bakin gwamnati, ya bayyana cewa tafiyar Gwamna zuwa aikin hajji ne ya kawo tsaiko a tsarin. Sai dai ya kara da cewa ana sa ran kafin watan Oktoba abubuwa za su daidaita, kuma shirin zai ci gaba kamar yadda aka tsara.
Ana sa ran wannan shiri zai kara karfafa harshen Larabci da kuma kwarewar malamai da dalibai a jihar Kano, tare da bunkasa ilimin addini da na zamani a tsakanin matasa.