ActionAid tare da haɗin gwiwar, Partnership Against Violent Extremism Network (PAVE), da PCVE-KIRH, ta gudanar da wani muhimmin taron kwanaki biyu a Kano domin tabbatar da sahihancin binciken da aka gudanar kan taswirar ci gaban al’umma da matsalolin tsattsauran ra’ayi, tare da samar da dabarun da za su kai ga shirin aiki na dogon lokaci..
Taron, wanda aka yi masa taken “Shaping Collective Action, Validation for Preventing and Countering Violent Extremism (PCVE) Strategies”, ya tattaro shugabanni daga sassa daban-daban ciki har da jami’an tsaro, masu rike da sarautun gargajiya, kungiyoyin farar hula, Mata da matasa daga yankuna daban-daban.
A yayin bude taron, jami’ar ActionAid da ke kula da shirin System and Structure Strengthening Approach against Radicalisation to Violent Extremism, Jamila Musa, ta bayyana cewa an gudanar da wannan bincike a kananan hukumomin Tudun Wada, Bebeji, Gwarzo, Bichi, Nasarawa da Karamar hukumar Gwale a Kano, da kuma al’ummomi goma sha biyu, domin gano ainihin abubuwan da ke haifar da tsattsauran ra’ayi da kuma hanyoyin magance su. Ta ce manufar taron ita ce tabbatar da sakamakon binciken tare da hada kan al’umma wajen bullo da shirin aiki mai dorewa.
A nasa jawabin, Jami'in da ya wakilci rundunar ‘yan sanda, DSP Hussaini Abdullahi, ya bayyana Kano a matsayin daya daga cikin jahohin da aka fi samun kwanciyar hankali a Najeriya, duk da kananan matsaloli irin su harkar daba. Ya ce daba babban laifi ne da ya shafi al’umma kai tsaye, kuma da hadin kan jama’a da bayanan sirri da suke samu, rundunar na daƙile wannan matsala yadda ya kamata.
Wasu daga cikin mahalarta taron, musamman jami’an tsaro da masu rike da sarautun gargajiya, sun yaba da sakamakon binciken da aka gabatar. Sun bayyana shi a matsayin wata hanya mai muhimmanci ta fahimtar matsalar daga tushe tare da shawo kan ta ta hanyar da ta dace. Sun kuma jaddada muhimmancin hadin kai tsakanin gwamnati, kungiyoyin farar hula da al’umma wajen yaki da tsattsauran ra’ayi da laifuffuka.
Taron ya kammala da kudirin samar da tsarin aiki wanda zai mayar da hankali kan inganta zaman lafiya, karfafa al’adu na fahimtar juna, da kuma bai wa matasa damar shiga ayyukan raya kasa domin rage yiwuwar fadawa cikin tsattsauran ra’ayi.