NDLEA ta Mika Kwayoyi Sama da Dubu 450 na Pregabalin ga NAFDAC a Kano

Hukumar hana sha da fataucin miyagun kwayoyi ta kasa (NDLEA) reshen Kano, ta mika kwayoyi sama da 450,000 na Pregabalin ga hukumar kula da ingancin abinci da magunguna (NAFDAC) domin gudanar da bincike da daukar matakan doka da ya dace da su.



Kwamandan hukumar a Kano, ACGN A. I. Ahmad, ya bayyana cewa an kama kwayoyin ne a cikin katuna 60, da aka boye cikin wata mota a kan hanyar Kano–Hadejia, ba tare da takardun izini ba.

Yayin karɓar kayan a Kano ranar Alhamis, Shugabar NAFDAC, Farfesa Mojisola Adeyeye, wadda Kasim Ibrahim, ko’odinetan hukumar a Kano, ya wakilta, ta yabawa NDLEA bisa tabbatar da bin yarjejeniyar fahimtar juna da gudanar da aiki tare da aka kulla a shekarar 2024. Ta kuma yi alkawarin ƙarfafa haɗin gwiwar don kare lafiyar al'ummar Kasar nan.

A cewarta, za a gudanar da binciken kwa-kwa da gwaje-gwaje kan kwayoyin, sannan a ɗauki matakin gurfanar da waɗanda ake zargi da laifin safarar su a gaban kotu.

Rahotanni sun nuna cewa kwayar Pregabalin na daga cikin magungunan da ake amfani da su wajen cututtuka daban-daban, amma kuma tana da hadarin jawo dogaro (addiction) idan aka yi amfani da ita ba bisa ƙa’ida ba, abin da ya sa gwamnati ke tsaurara matakan doka a kanta.

Previous Post Next Post