Shugaban kasa Bola Tinubu ya jaddada kudirin gwamnatin tarayya na yin amfani da fasahar zamani wajen karfafawa ‘yan Najeriya gwiwa.
Shugaba Tinubu ya bayyana haka ne a lokacin da yake kaddamar da aikin babbar hanyar Legas zuwa Calabar da kuma wasu manyan ayyukan tituna a Legas a karshen mako.
Shugaban ya umurci Ministan Ayyuka, Dave Umahi da sauran ministocin da ke sa ido kan ayyuka a fadin kasar, da su tabbatar da bin ka'idojin abubuwan cikin gida da horar da 'yan Najeriya.
Shugaban kasar ya amince da rawar da Ronald Chagoury ya taka wajen dakatar da ci gaban Tekun Atlantika da kuma ceto Victoria Island da Ikoyi, inda ya bukaci karin goyon bayan su wajen kawo ababen more rayuwa a Najeriya.
A nasa bangaren, Ministan Ayyuka, wanda ya ce an biya diyyar Naira Biliyan 18, ya kuma bukaci Shugaba Tinubu da ya umurci Dangote da BUA Cement su mika kashi 2 cikin 100 na tallace-tallacen su ga ma’aikatar.