Kungiyar a cikin wata sanarwa mai dauke da kwanan watan 30 ga watan Mayu, ta umurci sassanta na tarayya da su fara yajin aikin masana’antu daga ranar Lahadi.
Sai dai a wata sanarwa da kungiyar ta JUSUN ta fitar, ta umurci mambobinta na kasa baki daya da su dakatar da yajin aikin da suka shirya gudanarwa a yau.
Sanarwar ta bayyana cewa, an ba da wa’adin makonni biyu don baiwa hukumomin da abin ya shafa damar magance matsalolin da suka taso.
https://www.krmhausa.com/2025/06/shugaban-kasa-tinubu-ya-kaddamar-da.html
Hakan na zuwa ne bayan ministan kwadago da samar da ayyukan yi, Muhammad Dingyadi da sauran masu ruwa da tsaki suka gudanar da wasu tarurruka da shugabannin kungiyar a karshen mako.
Tags:
Labarai