Rikici Kan Yafewa Buhari: An Gurfanar da Matashi Bisa Zargin Fasa Baki

Matashin ya amsa laifin bugun wani mutum sakamakon sabani kan batun yafewa tsohon shugaban kasa marigayi Muhammadu Buhari.

Kano, Najeriya

Wani matashi mai suna Abubakar Hanbali ya gurfana a gaban kotun shari’ar Musulunci da ke Danbare, jihar Kano, bisa zargin duka da cin zarafi. 



Lamarin ya samo asali ne daga taƙaddama tsakaninsa da wani mazaunin unguwar Rijiyar Zaki, Musa Rabi’u Abubakar, dangane da batun yafewa marigayi tsohon shugaban kasa Muhammadu Buhari.

A cewar ƙunshin karar da aka shigar a ranar 15 ga Yuli, Musa ya bayyana cewa sun samu rashin jituwa da Abubakar Hanbali, wanda hakan ya kai ga bugunsa a baki, cin mutunci da fasa masa baki.

Da aka karanta masa laifinsa a gaban kotu, Abubakar ya amsa, yana mai cewa da ma malaman addini sun yi kira da a gafarta wa marigayin, amma shi ya nuna ƙin amincewa da hakan.

Mai shari’a Munzali Idris Gwadabe, ya bayar da umarnin a tsare wanda ake zargi a gidan gyara hali na tsawon kwanaki biyu, domin ci gaba da nazari da yanke hukunci.

Previous Post Next Post