Jami'an Rundunar hadin gwiwar ta Ƙasa da Ƙasa (MNJTF) a Kamaru sun kama wani wanda ake zargi da safarar makamai a kusa da garin Makary, wani yankin da ke kan iyakar tafkin Chadi, kamar yadda hukumomi suka sanarwa manema labarai a ranar Alhamis.
An gano wanda ake zargin, Abbaka Abba Djidda, mai shekaru 50, yayin wani aiki na musamman da aka gudanar bisa bayanan sirri da suka danganci alakar shi da wasu kungiyoyin safarar makamai da ke aiki a yankin tafkin Chadi.
A cewar wata majiya daga jami'an tsaro, an same shi da tarin makamai da ake zargin za a raba su ga kungiyoyin ‘yan ta’adda da ke kai hare-hare a wannan yanki.
Yankin tafkin Chadi, wanda tun da farko yake fama da matsalar ‘yan tawaye, an sanya jami'an rundunar hadin gwiwar tsaro tsakanin kasashen da ke cikin Rundunar (MNJTF), wanda ake gudanarwa don yakar ta’addanci, safarar makamai, da sauran laifuka tsakanin Ƙasa da Ƙasa.