Rundunar ‘yan sanda ta jihar Delta ta tabbatar da cafke mutum 184 da ake zargi da hannu a harkokin zamba ta hanyar intanet da kuma bada tallafi ga ayyukan ta’addanci, a wani sumame da aka gudanar a yankin Effurun da ke karamar hukumar Uvwie.
Majiyoyi daga ‘yan sanda sun bayyana cewa an kama wadanda ake zargin ne da yammacin ranar Litinin a unguwar Post Housing Estate da ke Effurun, bayan samun sahihan bayanai kan ayyukan wata kungiya da ke da alaka da aikata laifuka a Internet da kuma zargin bada tallafi ga ayyukan ta’addanci.
A cewar majiyar, DPO ofishin 'yan sanda na Ekpan, tare da jagorancin wani jami’in rundunar mai mukamin ASP, suka jagoranci tawagar jami'an da ta kai samame a misalin karfe 5:45 na yamma.
A lokacin wannan sumame, jami’an tsaro sun kama wani mutum mai suna Kelvin Odini, mai shekaru 33, wanda aka bayyana a matsayin babban wanda ake zargi, tare da wasu mutum 183 da ake zargin suna da hannu a aikata laifin.
Kayayyakin da aka gano a wajen su sun hada da:
Kwamfutoci (laptops) iri-iri har guda 273
iPad guda 1
Wayoyin salula guda 97
Cajin kwamfuta guda 9
Da na’urorin WiFi guda 2
Dukkan wadanda aka kama da kuma kayayyakin da aka kwato a hannunsu na hannun ‘yan sanda a shelkwatar da ke jihar.
Majiyar ta kara da cewa ana zurfafa bincike kan lamarin, yayin da ake ci gaba da kokarin cafke sauran mambobin kungiyar da suka tsere.