Kotun Shari’ar Musulunci Ta Yankewa Wani Matukin A Daidaita Sahu Hukuncin Dauri Kan Laifin Cin Amana da Zanba

 Kotun shari’ar Musulunci da ke unguwar Danbare a jihar Kano ta yankewa wani matukin adaidaita sahu, Mansir Lawan, hukuncin daurin shekara daya da wata uku, bayan samunsa da laifin siyar da mashin da aka ba shi  a matsayin haya purchase.



An tuhumi Mansir Lawan da laifin cin amana da zanba, laifuka da suka saba da sashi na 202 da 206 na kundin dokokin shari’ar Musulunci na jihar Kano.

A cewar mai kara, Alasan Ahmad, wanda ya shigar da korafi a ofishin 'yan sanda a ranar 21 ga watan Yuli, ya bayyana cewa ya ba da babur din adaidaita sahu ga Mansir Lawan dan unguwar Gaida Yankusa bisa tsarin haya purchase, inda zai biya ₦850,000 a tsarin mataki-mataki har mashin din ya zama nasa.

Sai dai ya ce Mansir ya biya kashi na farko ₦480,000, ya ki cikawa sannan kuma ya siyar da mashin din gaba daya, sannan ya ɓace ba tare da sanarwa ba.

Bayan shigar da ƙunshin tuhuma daga mai gabatar da kara, Lauyan gwamnati Musabahu Usman, an nemi kotu ta yanke hukunci nan take.

Alkalin kotun, Mai shari’a Munzali Idris Gwadabe, ya yanke masa hukuncin daurin shekara daya ko tarar ₦30,000 kan laifin cin amana, da kuma daurin wata uku ko tara ta ₦10,000 kan laifin zanba, tare da umarnin biyan kuɗin ranko ₦370,000 ga mai karar.

Previous Post Next Post