Daga wakilin mu - Ado Danladi Farin Gida, Kano
Gwamnatin Jihar Kano ta ƙaddamar da shirin dashen bishiyoyi miliyan biyar da dubu dari biyar (5.5 million) domin daƙile ƙwararowar hamada da kuma inganta lafiyar muhalli a fadin jihar.
Gwamnan jihar, Injiniya Abba Kabir Yusuf, ne ya jagoranci kaddamarwar a kauyen Dan Bawa da ke karamar hukumar Makoda, inda ya bayyana cewa za a raba bishiyoyin ne ga kananan hukumomi 44 da ke fadin jihar.
A cewar gwamnan, “Za a ba da bishiyoyin kyauta ga manya da ƙananan makarantu, masallatai, ma’aikatu da gidajen al’umma don karfafa shirin dasa bishiyoyi da kuma tabbatar da kyakkyawan yanayi mai dorewa.”
Gwamna Abba Kabir ya yabawa Kwamishinan Muhalli da sauyin yanayi na jihar, Dr. Dahiru Hashim, bisa jajircewarsa wajen tsarawa da kuma aiwatar da wannan muhimmin shiri na kare muhalli da inganta rayuwar al’umma.
A nasa jawabin, Sarkin Kano, Khalifa Muhammadu Sanusi II, wanda ya samu wakilcin Hakimin Gwarzo, Alhaji Bello Abubakar, ya bukaci gwamnatin jihar ta farfado da dokar hana sare bishiyoyi a fadin Kano. Ya ce hakan zai taimaka wajen kare dazuka da kuma dakile barazanar da kwararowar hamada ke yi ga muhalli da rayuwar al’umma.