Wani sanannen dan gwagwarmaya kuma mai rajin kare hakkin masu bukata ta musamman, Injiniya Abdul Haruna, ya bukaci gwamnatin tarayya da ta dauki matakan gaggawa wajen kare hakkin wadanda ke fama da larural laka a Najeriya, tare da kafa wata doka da za ta kula da bukatunsu na musamman.
Injiniya Haruna, wanda ya taba rike shugabancin kungiyar masu lalural a baya a Najeriya (SCIAN), reshen Kano, ya mika wannan bukata cikin wata takarda da ya fitar a ranar Asabar.
A cewarsa, akwai bukatar saka masu fama da lalurar ta laka cikin kundin tsarin mulkin kasa da kuma samar da wata sabuwar doka da za ta fayyace hakkokinsu da yadda gwamnati za ta tallafa musu. Ya ce, “Ko da yake an saka su a cikin rukuni na masu bukata ta musamman, amma su rukuni ne dake bukatar wata kulawa ta daban, kama daga magunguna da suke amfani da shi, bukatar sake farfaɗowa da kuma tallafin zamantakewa.”
Ya bayyana cewa a Jihar Kano kadai, sama da mutane 4,000 ke samun lalurar laka duk shekara, mafi yawanci daga hadurran ababen hawa. Haruna ya ce wannan al'amari na bukatar kulawa ta musamman daga matakin gwamnatin tarayya.
Daga cikin shawarwarin da ya gabatar akwai:
-
Kafa sabuwar doka a 2025 wacce za ta halasta gina cibiyoyin jinya a sassa daban-daban na kasar nan.
-
Kafa Hukumar Kula da Masu Lulurar Lakaa ta Kasa (NSCIC) da za ta rika lura da shirye-shiryen da suka shafi masu lalurar laka da gudanar da bincike.
-
Samar da Tsarin Dabarun Kulawa da Masu Lalurar Laka na Ƙasa, wanda zai zayyana manufofi da hanyoyin aiwatar da su.
Baya ga haka, Injiniya Haruna ya bukaci gina cibiyoyin jinya ta musamman (rehabilitation centers) a kowace yanki shida na siyasa a Najeriya, tare da cikakkun kayayyakin aiki kamar na tiyata, motsa jiki, kulawar kwakwalwa da koyar da sana'o’i.
Haka zalika, ya bukaci a saka magungunan masu lalurar laka cikin tsarin inshorar lafiya ta kasa (NHIS) domin su zama masu araha da saukin samu.
A bangaren ilimi da ci gaban rayuwa, ya nemi gwamnati ta ba da ilimi kyauta da horon sana’a ga wadanda suka samu wannan matsalar da kuma kula da su, tare da samar da ayyukan yi da shirye-shiryen tallafi domin rage dogaro da iyali da al'umma.
Haruna ya kuma yi kira ga gwamnati da ta tabbatar da cewa gine-gine da hanyoyin sufuri sun dace da masu nakasa, tare da wayar da kan al'umma domin dakile wariya da nuna kyama.
Don kara wayar da kai, ya bada shawarar a ayyana ranar 5 ga Satumba a matsayin Ranar Wayar da Kan Jama’a Game da Masu lalurar laka a Najeriya.
A karshe, ya bukaci a kara karfafa dokokin hana wariya a fannonin ilimi, lafiya da aikin yi, yana mai cewa hakan zai bai wa masu fama da wannan lalura damar rayuwa cikin martaba da walwala kamar sauran 'yan kasa.