Haɗaɗɗiyar Ƙungiyar Shugabannin Manyan Makarantun Legal ta Najeriya ta Zaɓi Farfesa Jakada a Matsayin Shugaban ta

Hadaddiyar kungiyar shugabannin makarantun Shari’a (Legal) ta Najeriya ta zabi Farfesa Abubakar Jakada a matsayin sabon shugabanta na kasa.



Wannan naɗi ya biyo bayan taron da kungiyar ta gudanar a ranar Litinin, 25 ga Agusta, 2025, a Kwalejin Shari’a da  addinin musulunci ta Malam Aminu Kano, wato Legal.

Mai magana da yawun kwalejin, Dr. Salisu Marafa Sagagi, ya bayyana cewa zaben ya samu amincewar mambobin kungiyar baki daya, yana mai cewa wannan shi ne karo na farko da aka yi irin wannan zabe tun bayan kafuwar kungiyar shekaru 23 da suka wuce.

Farfesa Jakada, a sakon godiyarsa, ya nuna jin dadinsa kan wannan amincewa, tare da tabbatar da cewa zai yi duk mai yiwuwa don tabbatar da cigaba da nasarar kungiyar da ma makarantun da take wakilta.

Previous Post Next Post