Kano Ta Jaddada Kudirin ta na Ci gaba da Ƙarfafa Manyan Makarantu

Ado Danladi Farin Gida, Kano

Gwamnatin Jihar Kano ta sake nanata aniyarta na inganta manyan makarantu da ke fadin jihar domin ci gaba da bunkasar ilimi.



Mataimakin Gwamnan Jihar Kano kuma Kwamishinan Ilimi mai zurfi, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, ne ya bayyana haka yayin bude taron shekara-shekara na 48 na shugabannin Kwalejojin Shari’ar Addinin Musulunci na Najeriya (COPCLIS), da aka gudanar a Kwalejin koyon shari'ar Addinin Musulunci ta Aminu Kano (AKCILS).

Kwamared Gwarzo ya yaba wa Kungiyar COPCLIS bisa jajircewarsu wajen bunkasa ilimi, yana mai cewa tattaunawarsu da hangen nesansu sun taka muhimmiyar rawa wajen tsara tsarin ilimi a Najeriya.

Ya jinjinawa shugaban Kungiyar COPCLIS mai barin gado bisa nasarorin da ya cimma, musamman sauya matsayin shirin Diploma na Shari’a daga Ordinary zuwa National Diploma da kuma shigar da shirin cikin tsarin JAMB na shekarar karatu ta 2024.

Mataimakin Gwamnan ya taya sabon Shugaban kungiyar COPCLIS, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, murna tare da bukatar ya ci gaba da kare martabar ofishin da ya karba da kuma cimma manufofin taron.

Dangane da matsalolin gine-gine, Kwamared Gwarzo ya tabbatar da cewa gwamnati ta lura da matsalolin da ake fuskanta, kuma tana daukar matakai domin magance su.

Ya kara da cewa dokar da za ta mayar da AKCILS cikakkiyar Kwalejin Ilimi na hannun Ma'aikatar Shari’a don duba ta, a matsayin wani mataki na goyon bayan ci gaban ilimi a jihar.

A nasa jawabin, sabon Shugaban kungiyar ta COPCLIS kuma Provost na AKCILS, Farfesa Balarabe Abubakar Jakada, ya nuna godiyarsa ga gwamnatin jihar bisa tallafin da ta bayar, ciki har da gyaran dakin taro da wuta ta lalata da kuma daukar nauyin tantancewar NBTE da aka yi kwanan nan.

Ya bukaci karin taimako wajen gyaran dakunan karatu da suka lalace da kammala sauran muhimman gine-gine tare da jaddada bukatar shigar da dukkan kwalejojin cikin shirin TETFund.

Taron ya kuma kunshi bayar da kyaututtukan girmamawa ga fitattun mutane ciki har da Gwamnan Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, Mataimakin Gwamna, Kwamared Aminu Abdulsalam Gwarzo, Kwamishinan Ilimi, Gwani Dr. Ali Haruna Makoda, da Kwamishinan Kimiyya da Fasaha, Dr. Yusuf Ibrahim K/Mata.

Previous Post Next Post