Daga Ado Danladi Farin Gida
Kotun Majistire da ke Koki 'yan Awaki a Jihar Kano ta bayar da umarnin a tsare wasu mutane takwas a gidan tarbiyya da gyara hali, bisa zargin hannu a kone gidan wani Fulani a kauyen Sakaratsa, da ke karamar hukumar Rimin Gado.
Wadanda ake zargin sun hada da Garzali Garba, Sa’idu Umaru, Shamsuddeen Ayuba da Amina Umar. Ana zarginsu da laifukan hada kai wajen aikata laifi, kutse ba bisa ka’ida ba, barazana, kona gida da kuma mallakar muggan makamai.
A cewar mai gabatar da kara, ranar 8 ga watan Yuni, wadanda ake zargin tare da wasu da har yanzu ba a kama su ba, sun kutsa gidan wani Alhaji Bello a garin Sakaratsa dauke da makamai, inda suka banka masa wuta. Gidan ya kone kurmus tare da lalata kayayyaki da suka hada da mashin da kudinsa ya kai Naira miliyan daya da dubu dari shida, wasu kudadde da kuma kayan amfani na gida.
Bayan an karanta musu tuhume-tuhumen a gaban kotu, wadanda ake zargin sun musanta laifin. Sai dai lauyar gwamnatin, Hajara Ado Sale, ta bukaci kotu da ta dage shari’ar zuwa wata rana domin neman shawara daga Ma’aikatar Shari’a, duba da cewa tuhumar kona gida ba ta cikin hurumin wannan kotu.
Mai shari’a Ibrahim Faruk ya amince da bukatar, inda ya bayar da umarnin a ci gaba da tsare wadanda ake zargin a gidan gyara hali har sai an samu umarni daga Ma’aikatar Shari’a.
Da yake tofa albarkacin bakinsa bayan zaman kotun, wanda lamarin ya shafa, Alhaji Bello, ya bayyana cewa ya yi asarar dukiya mai tarin yawa, yana mai jinjinawa Ma’aikatar Shari’a bisa daukar matakin da ya dace.
Shi ma jagoran kungiyar Fulani ta Fuldon a yankin, Ibrahim Baba, ya yaba da matakin da kotun ta dauka, yana mai cewa hakan na kara tabbatar da cewa doka na aiki a kasa.