Hukumar ta ce dole ne a biya iyalan mamata diyya, idan direban ya yi tuki ba bisa ka’ida ba – ko da ya mutu
Daga Ado Danladi Farin Gida, Kano
Hukumar Kare Hakkin Bil’adama ta Kasa da Kasa (International Human Rights Commission – IHRC) ta bayyana cewa za ta tabbatar da cewa an biya diyya ga iyalan duk wani fasinja da ya mutu a hatsarin mota da aka yi hatsari ta hanyar aron hannu ko tuƙin ganganci.
Wannan jawabi ya fito ne daga Ambassador Dr. Abubakar Rabo, mataimakin shugaban hukumar a Najeriya, yayin wata ganawa da manema labarai a ofishinsa da ke kan titin Court Road, Kano.
Dr. Rabo ya bayyana cewa hukumar ta samu izini daga Majalisar Dinkin Duniya na bibiyar irin waɗannan al’amurra tare da tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa.
"Ko direban ya mutu, za mu tabbatar da cewa iyalansa sun biya diyya ga iyalan fasinjojin da suka mutu a sakamakon hadarin," in ji shi.
Ya ce lokaci ya yi da za a dakile gangancin da direbobi ke yi a hanyoyi, wanda ke janyo asarar rayuka da jefa iyalai cikin halin damuwa da rashin kulawa daga gwamnati ko hukumomin da abin ya shafa.
A cewar Dr. Rabo, IHRC za ta fara gurfanar da duk wani direba da aka samu da laifin tuki da aron hannu ba bisa ka’ida ba, musamman idan hakan ya janyo mutuwa.
Kira Ga FRSC da Kungiyoyin Direbobi
Ya bukaci Hukumar Kiyaye Hadurra ta Kasa (FRSC) da kuma kungiyoyin direbobi da su tashi tsaye wajen fadakar da mambobinsu kan illar aron hannun a yayin tafiya da kuma tukin ganganci.
"A mafi yawancin lokuta, aron hannun da rashin bin doka ke zama silar manyan hadurra, musamman a titunan birane da kauyuka," in ji shi.
Dr. Rabo ya bayyana bakin cikinsa game da wata musifa da ta rutsa da wasu ’yan wasan kwallon kafa da suka wakilci jihar Kano, inda suka mutu yayin da suke daf da shiga birnin Kano sakamakon irin wannan tukin da aron hannun.
“Wannan dabi’a ta tuki da aron hannu na kashe dimbin rayuka, kuma yanzu lokaci ya yi da za a tunkari matsalar da hannu biyu,” in ji shi.