Hukumar Hadejia Jama’are Ta Bukaci Manoma Su Yi Amfani da Ruwa Ta Hanyar Da Ta Dace

 Kano – Hukumar kula da madatsar ruwa ta Hadejia–Jama’are ta ja hankalin manoma masu amfani da ruwa su rika yin amfani da shi yadda ya kamata domin tabbatar da dorewar noman su.



Shugaban sashen injiniyanci na hukumar, Sani Yakubu Danladi, wanda ya wakilci manajan ayyuka a hukumar, Yakubu Sani, ne ya bayyana haka a yayin kaddamar da sababbin shugabannin ƙungiyar manoma masu amfani da ruwa a jihar Kano.

A cewarsa, hukumar na samar da ruwa daga madatsar zuwa manyan koguna, yayin da ƙungiyar manoma ke da alhakin rarraba ruwan cikin adalci ga ‘yan uwansu manoma a ƙasa.

“Mun kaddamar da shugabanni ne domin tabbatar da cewa ruwan da muke samarwa daga madatsar ya isa ga kowane manomi yadda ya dace. Idan an yi amfani da ruwa bisa adalci, dukkannin manoma za su ci gajiyar aikin noma ba tare da matsala ba,” in ji shi.

A nasa ɓangaren, sabon shugaban ƙungiyar manoma masu amfani da ruwa a Kano, Mustapha Adamu Mudawa, ya bayyana cewa tsarin zaɓen shugabanni ana gudanar da shi duk bayan shekaru huɗu.

Ya ce a bana aka zaɓe shi bisa jajircewa da ƙoƙarin da suka nuna wajen gudanar da ayyukan ƙungiyar. Ya kuma yi alkawarin tabbatar da cewa dukkan manoma za su sami isasshen ruwa domin gudanar da ayyukan noma cikin nasara.

“Mun yi alkawarin yin aiki tuƙuru tare da sauran shugabanni domin tabbatar da cewa babu wani manomi da zai koka kan rashin ruwa. Za mu tabbatar da adalci wajen rarraba ruwa domin inganta noman al’umma,” in ji Mudawa.

Previous Post Next Post