Kotu Ta Yanke wa Matashi Hukuncin Daurin Sati Biyu Kan Zubar da Shara a Kano

Ado Danladi Farin Gida- Kano


Wata kotu a jihar Kano ta yanke wa wani matashi mai suna Yusuf Ishak, hukuncin daurin sati biyu a gidan gyara hali da tarbiyya, tare da rubuta takardar neman afuwa ga hukumar kwashe shara ta jihar Kano.



An gurfanar da Yusuf ne a gaban Kotun Majistire mai lamba 7, bisa tuhume-tuhume da suka hada da zubar da shara a kusa da gadar Dangi da ke kan titin Kano–Zariya, da kuma hana ma’aikatan hukumar yin aikinsu tare da cin zarafinsu.

Bayan an karanta masa kunshin tuhume-tuhumeN, Yusuf ya amsa laifinsa. Daga nan mai shari’a Halima Wali, ta yanke masa hukuncin daurin sati biyu a gidan gyara hali da tarbiyya, ko kuma biyan tarar naira dubu goma sha biyar (₦15,000). Haka kuma, ta umurce shi da ya rubuta takardar neman afuwa ga hukumar kwashe shara.

Bayan kammala zaman kotun, shugaban hukumar kwashe shara ta jihar Kano, kuma shugaban kula da tsaftar muhalli, Dr. Muhammad S. Khalid, ya bayyana irin dokar da Yusuf ya karya. da suka hada da bata muhalli ta hanyar zubar da shara akan titi sannan ya ci zarafin ma'aikaci tare da cewa zai je har hukumar ya sake zubar da shara sannan ya baikata ikirarin da yayi,

Daga nan sai shugaban ya gargadi jama’a kan zubar da shara akan tituna, ya na mai cewa hukumar ba za ta yi shiru  kan masu karya doka ba, inda ya ce:

"Za mu fito da kotun tafi-da-gidan-ka domin hukunta duk wanda aka samu da laifin zubar da shara a tituna da unguwanni."

Previous Post Next Post