Mata Masu Juna Biyu 150 Sun Amfana da Shirin Taimakon Lafiya a Dawakin Kudu

Ado Danladi Farin Gida, Kano

A karamar hukumar Dawakin Kudu, mata masu juna biyu 150 sun samu shiga shirin taimakekeniyar lafiya na jihar Kano, wanda zai rika kula da lafiyarsu tun daga watanni biyu na juna biyu har zuwa bayan haihuwa.



Shugabar hukumar, Dr. Rahila Mukhtar, wadda ta samu wakilcin Daraktan Mulki a ma’aikatar lafiya, Amina Sani Usman, ta bayyana cewa wata cibiya mai zaman kanta ta dauki nauyin yiwa mata 50 rajista a hukumar. Daga nan ne gwamnatin jihar Kano ta kara da mata 100, wanda ya kai adadin 150 da za a kula da lafiyarsu.

Ta shawarci Matan da su rika ziyartar asibitocin da aka yi musu rajista akai-akai, domin tabbatar da samun cikakken kulawa da lafiyar su da ta jariran da suke dauke da su.

Shima shugaban cibiyar mai zaman kanta da ke Dawakin Kudu, Aminu Bala Sarkin Dawaki, ya ce sun samu goyon bayan al’umma da shugabannin karamar hukumar wajen tallafawa Mata 50, inda aka biya kuɗi har naira dubu dari shida domin tabbatar da nasarar shirin.

Previous Post Next Post