Uba Sani ya Kaddamar da Aikin Titin Lere, Ya Ce Zai Kawo Sauyi ga Manoma

Gwamnan jihar Kaduna, Sanata Uba Sani, ya kaddamar da aikin gina titin Kayarda–Tasha–Masakawa–Dan Alhaji da ke karamar hukumar Lere, yana mai cewa wannan aiki zai bunkasa tattalin arzikin karkara, rage gibin ci gaban da ke tsakanin birane da kauyuka, da kuma samar da ayyukan yi.



Lere na daga cikin muhimman wuraren noma a Najeriya, musamman wajen samar da masara, tumatir, wake, da rake.

“Haɗaɗɗiyar hanya a Karamar hukumar Lere za ta inganta rayuwar manoma, sannan ta buɗe sabbin damarmaki na kasuwanci, ta ƙara samar da haɗin kai tsakanin al'ummar kauyukan, da kuma tabbatar da dorewar arziki,” in ji gwamnan.

Ya kuma bayyana cewa Shugaban kasa Bola Tinubu ya amince da gaggauta farfado da aikin Pambegua–Saminaka–Jos Road, kana kuma ana nazarin gyaran titin Saminaka–Kano  saboda muhimmancin ta ga harkokin kasuwanci.

Sarkin Lere, Alhaji Umar Suleiman, ya ce aikin titin ya zo a dai-dai lokacin da al'umma ke bukatar shi sosai:

“Shekaru da dama manoma suna fama wajen kai kayan gona kasuwa. Wannan hanya za ta sauya wancan labarin, kuma ta dawo musu da fata.”

Mazauna yankin suma sun nuna farin ciki.

Ibrahim Zubairu, wani mai rike da sarautar gargajiya  a Kayarda, ya ce:

“Za mu daina asarar kayan gona saboda jinkiri da ake samu da kuma matsalar hanyoyi marasa kyau. Yanzu za mu kai tumatir da masara kasuwa cikin lokaci.”

Shi kuwa Lawal Gambo ya ce labarin gyaran manyan hanyoyin tarayya ya tabbatar musu da cewa gwamnati na sauraren koke-kokensu.

Previous Post Next Post