Akalla Mutane 10 Sun Rasu Sakamakon Harin Bam a Borno

Wani da ake zargin dan kunar bakin wake ne daga kungiyar Boko Haram ya hallaka akalla mutane 10 a wani mummunan hari da ya auku a kasuwar kifi da ke karamar hukumar Konduga, Jihar Borno.



Lamarin ya faru ne da daren Juma’a, lokacin da mutumin ya shiga kasuwar, sannan ya tayar da wani bam a cikin taron jama’a.

Wannan bayani ya fito ne daga wani mai sharhi kuma masanin kan harkokin tsaro, Zagazola Makama, da ya wallafa a dandalin sa X (tsohuwar Twitter) a ranar Juma’a.

A cewar Makama, fashewar ta yi sanadiyyar mutuwar fararen hula 10, yayin da wasu bakwai suka jikkata a wurin da abin ya faru.

“Dan kunar bakin waken shi ma ya mutu a fashewar,” in ji Makama.

Bayan aukuwar lamarin, sojoji da jami’an agajin gaggawa sun garzaya wurin domin ceto rayuka da kuma daukar matakin gaggawa.

An garzaya da wadanda suka jikkata zuwa cibiyar lafiya mafi kusa domin samun kulawa.

Makama ya kara da cewa jami’an tsaro sun killace yankin domin hana yiwuwar sake kutse daga wasu da ake zargi da shirin kai irin wannan hari.

Previous Post Next Post