An Sake Kai Wani Sabon Hari A Garin SGF Akume, Kwana Biyu Bayan Ziyarar Tinubu

Ana zargin wasu da kai mummunan hari a garin Wannune da ke karamar hukumar Tarka a Jihar Benue — mahaifar Sakataren Gwamnatin Tarayya (SGF), Sanata George Akume.



Rahotanni sun ruwaito cewa harin ya yi sanadin mutuwar mutane da dama tare da jikkata wasu da yawa, lamarin da ya faru cikin dare, kwanaki biyu kacal bayan ziyarar shugaban Kasa Bola Ahmed Tinubu, zuwa jihar domin duba matsalar tsaro da ke kara tabarbarewa.

Wani mai hidimtawa Kasa (NYSC) da ke aiki a yankin ya bayyana halin da ake ciki a matsayin na “tsoro da firgici”, yana mai rokon 'yan Najeriya su yi addu’a tare da neman agajin gaggawa daga hukumomin tsaro.

“Dukkanmu mun gudu cikin dokar daji don ceton rayukanmu. Mahara sun addabi garin yanzu,” in ji shi cikin muryar neman agaji.

Sabon harin na zuwa ne a daidai lokacin da ake kokarin kwantar da tarzoma da kawo karshen tashin hankali a jihar, musamman bayan kisan gillar da aka yi a Yelewata, karamar hukumar Guma, inda aka kashe sama da mutane 200 — lamarin da ya haifar da kakkausar suka da bacin rai a fadin kasar.

A yayin ziyararsa, Shugaba Tinubu ya gana da manyan shugabanni da masu ruwa da tsaki a jihar, inda ya bayar da umarni ga Babban Sufeto rundunar‘Yan Sanda da Shugaban Hafsoshin Tsaro su kamo wadanda ke da hannu cikin kisan.

Sai dai, harin da aka kai a Tarka ya jefa tambayoyi kan tasirin wannan ziyarar da kuma ingancin matakan tsaro da aka sanar.

Previous Post Next Post