Mai Martaba Sarkin Gwoza, Alhaji Mohammed Shehu Timta, ya karyata rahotannin da ke cewa ‘yan ta’addan Boko Haram sun kai hari a garin Gwoza da ke Jihar Borno.
Sarkin ya bayyana cewa rahotannin da suka janyo firgici a tsakanin al’umma ba gaskiya bane, an shirya ne domin tada hankali da yaudarar jama’a.
Martanin Sarkin ya biyo bayan labarin firgici da ya karade garin Gwoza a ranar Juma’a, bayan jin karar harbe-harbe daga nesa da garin, jim kadan bayan kammala sallar Juma’a. Wannan lamari ya haifar da fargabar yiwuwar wani sabon hari, la’akari da cewa Gwoza na kan iyaka da dajin Sambisa da tsaunukan Mandara, wadanda ake danganta su da zama mafakar ‘yan ta’adda.
“Banji dadin yadda mutane suka rika gudu suna cewa Boko Haram sun kawo hari Gwoza. Ba wani abu makamancin haka,” in ji Sarkin a ganawar da yayi da manema labarai.
Ya bayyana cewa binciken farko da aka gudanar tare da hadin gwiwar kwamandan rundunar sojin da ke yankin ya tabbatar da cewa babu wani hari ko artabu da aka samu tsakanin sojoji da ‘yan ta’adda a cikin garin Gwoza.
Sarkin ya amince cewa an ji karar harbi daga wajen gari, amma ya jaddada cewa hakan ba yana nufin akwai wani hari kai tsaye ga al’ummar gari ba.
Sai dai kuma ya ce, rahotanni tushe sun nuna cewa wasu mutane hudu da ke sanye da bakaken kaya—wadanda ake zargi 'yan kungiyar Boko Haram ne—an hango su suna kutsa kai cikin sansanin ‘yan gudun hijira.
Amma ya jaddada cewa har yanzu ba a tabbatar da sahihancin rahoton ba.
Ya kara da cewa, “Sojoji na ci gaba da gudanar da bincike mai zurfi domin tabbatar da cewa ba a samu kutsen ba. Dokar hana fita da aka saka na nufin taimaka wa jami’an tsaro su gudanar da aikinsu cikin kwanciyar hankali, da kuma kare al'umma daga firgici marar tushe.”