Alhazai sun fara isa Mina a Laraba nan, 8 ga watan Dhul Hijjah, shekarar 1446 bayan Hijira, domin faraTarwiyah, alamar fara ibadun Hajji na shekarar 2025.
Kusan kashi 64% na alhazan suna Mina, yayin da sauran kashi 36% suka wuce kai tsaye zuwa Arafat don yin babban rukuni na Hajji, kafin su dawo Mina ta Muzdalifah domin yin kwanakin Tashreeq.
Mina na da tazarar kimanin kilomita bakwai (7 km) daga Masallacin Harami a Makka, kuma tana da muhimmancin a addini da tarihi .
A nan ne Annabi Ibrahim (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya jefi shaidan kuma ya yi niyyar bada Dansa Isma'il a matsayin hadaya, wani aiki da Annabi Muhammad (tsira da amincin Allah su tabbata a gare shi) ya sake tabbatar da shi a lokacin Hajjin bankwansa.
Mina na dauke da muhimman wurare kamar Jamarat uku (ginshiƙan jifar shaidan) da Masallacin Al-Kheef, wanda ake kyautata zaton annabawa da dama sun yi salla a cikinsa.
Hakanan, Mina na da matsayi na siyasa, domin a nan ne aka yi rantsuwar Aqabah ta farko da ta biyu, inda Musulmi daga Yathrib (yanzu Madinah) suka yi mubaya’a ga Annabi Muhammad. Don tunawa da wadannan abubuwan tarihi, Khalifan Abbasiyawa Abu Ja’far Al-Mansur ya gina Masallacin a shekarar 144 AH kusa da wurin.
Duba da mahimmancin ayyuka na Mina, hukumomin Saudiyya sun fadada ayyuka da kayayyakin more rayuwa. An samar da cikakken tsari na tsaro, lafiya, abinci da sufuri don karɓar alhazai.Hukumomin gwamnati sun jaddada kudurinsu na tabbatar da tsaron lafiyar alhazai da samar da yanayi mai cike da nutsuwa domin su gudanar da ibadunsu cikin Aminci.
Shirye-shiryen da gwamnatin Saudiyya ta yi domin Hajjin shekarar 1446 AH na nuna jajircewarta wajen karɓar miliyoyin alhazai a kowace shekara, tana mai da hankali kan inganci, tsaro, da tabbatar da anyi cikakkiyar ibada.