GMBNI Ta Koka da Rasuwar Almajirai a Kaduna, Ta Bukaci Daukar Mataki


Gidauniyar Inganta Rayuwar ’Yan Najeriya tun daga Matakin Karkara (GMBNI) ta bayyana alhini da matuƙar jimaminta kan mummunar rasuwar almajiran da kasa ta rufta musu a jihar Kaduna.



Shugabar gidauniyar a Najeriya, Ambasada Dakta Fatima Mohammed Goni, ita ce ta bayyana hakan yayin  zantawar ta da KRM Hausa, inda ta yi kira ga duk masu ruwa da tsaki da su dauki matakan gaggawa domin hana faruwar irin wannan annoba a nan gaba.

Ta kara da cewa:

“Muna kira ga mahukunta da su ƙara zage damtse wajen sake duba harkar almajiranci, ta hanyar haɗin gwiwa da kungiyoyin sa kai. Wannan zai taimaka wajen tabbatar da cewa irin wannan bala’i bai sake faruwa ba. Gwamnatin tarayya ta riga ta fara gyaran tsarin karatun almajiranci karkashin hukumar NCAOOCES.”

Ambasada Goni ta kuma bukaci Alarammomi, malamai da iyaye da su sanya idanu sosai kan wuraren da almajirai ke ziyarta, musamman irin waɗanda ba su da cikakken tsaro ko gini mai ƙarfi.

A ƙarshe, shugabar gidauniyar ta miƙa sakon ta’aziyya ga iyalan almajiran da suka rasu, malamansu, da kuma gwamnatin jihar Kaduna, tana mai addu’ar Allah ya jikansu da rahama.

Rundunar ’yan sandan jihar Kaduna ta tabbatar da mutuwar almajirai 11, yayin da wasu 7 ke ci gaba da samun kulawar likitoci a asibiti. Lamarin ya faru ne a kauyen ’Yar-Doka, ƙaramar hukumar Kubau, inda wata kasa  a kududdufi ta rufta tare da binne yaran da ke wasa a wurin.

Previous Post Next Post