Kungiyar Dispute Resolution and Development Initiative (DRDI) ta bayyana jimami da alhini matuka bisa rasuwar wasu Matasan ’yan wasan daga Jihar Kano da suka rasa rayukansu a wani mummunan hatsari da ya afku kwanan nan.
A cikin wata sanarwa da ta fitar, kungiyar tare da Kwamitin Amintattunta, Ma’aikata, da Babban Daraktan ta Dr. Mustapha Muhammad Yahaya, ta ce wannan lamari babban rashi ne da ya girgiza zukata, musamman ganin cewa matasa ne da ake sa rai a kansu wajen gina kasa a nan gaba.
DRDI ta na mika ta’aziyya ga Mai girma Gwamnan Jihar Kano, Alhaji Abba Kabir Yusuf, da Mai Martaba Sarkin Kano, Alhaji Muhammadu Sanusi II, da kuma iyalan wadanda abin ya shafa, tana mai addu’ar Allah Ya ba su hakurin jure wannan babban rashi.
Sanarwar ta kara da cewa daga cikin wadanda suka rasa rayukansu akwai Matasa da ke da nauyin kula da iyalansu, inda kungiyar ta yi kira ga Gwamnatin Jihar Kano da ta dauki matashi daya daga kowanne daga cikin iyalan da lamarin ya shafa aiki a cikin gwamnati, a matsayin tallafi da rage radadin rashin da suka yi.
Dr Mustapha ya ce “ya na mai kira ga Gwamnatin Kano da ta duba yiwuwar daukar matashi daya – Mace ko Namiji – daga kowanne daga cikin iyalan domin taimaka musu wajen shawo kan matsin tattalin arziki da wannan rashi zai iya haifarwa,”
A karshe, DRDI ta yi addu’ar Allah Ya jikan wadanda suka rasu, Ya sa aljannar firdausi ita ce makomar su, tare da karfafa zukatan iyalansu da sauran al’umma da wannan rashi ya shafa.