Dubban Musulmi sun taru a Dutsen Arafat da safiyar Alhamis don gudanar da addu’o’i da karatun Al-Qur’ani a wani babban matakin aikin Hajji, yayin da hukumomin Saudiyya suka shawarci mahajjata da su guji fitowa a lokutan da rana ta kwallare saboda zafi mai tsanani.
Tun kafin ketowar alfijir, alhazai daga sassa daban-daban na duniya suka fara taruwa a kan tsaunin Arafa da kuma filayen da ke kewaye da shi — inda Annabi Muhammadu (SAW) ya yi hudubarsa ta karshe kafin rasuwarsa.
Wasu daga cikin mahajjatan sun iso da wuri domin su amfana da sanyin safiya, dauke da lema don kare kansu daga rana. Amma da dama daga cikinsu za su ci gaba da kasancewa a wurin har zuwa yamma, suna gudanar da addu’o’i da karatun Al-Qur’ani – wanda ke zama daya daga cikin mafi girman matakai na aikin Hajji.
Bayan faduwar rana, za su nufi Muzdalifah – wani wuri da ke tsakiyar hanyar Arafat da Mina – inda za su kwana da dare su tsinci ƙananan duwatsu domin gudanar da jifan shaidan a gobe.