Hukumar Kiyaye Hadurran ta Ƙasa (FRSC) reshen jihar Kano ta bayyana cewa ta samar ada kotun tafi da gidan ka (mobile courts) tare da jami’ai 1,889 domin saukaka zirga-zirga da tabbatar da tsaron hanyoyi yayin bukukuwan Sallah Karama (Eid-el-Fitr) a jihar Kano.
Mai magana da yawun rundunar, Abdullahi Labaran, ya ce an tsara kotunan tafi-da-gidanka domin gudanar da shari'o'in da suka shafi karya doka kai tsaye a wuraren da hadurra suka faru. Wannan mataki zai taimaka wajen hanzarta shari’a da kuma rage yawaitar laifukan da direbobi ke aikatawa a lokacin da hanyoyin ke cike da jama'a.
A cewarsa, kotunan tafi-da-gidanka sun kunshi alkalai da ma’aikatan Shari'a, kuma za su yi aiki a manyan titunan da ke da cunkoso da kuma wuraren da ake yawan samun hadurra.
Labaran ya kara da cewa jami’ai 1,889 da suka hada da masu sintiri, masu sa ido, da sashen kula da zirga-zirga za su kasance a muhimman wurare domin gudanar da aikin kulawa da zirga-zirga da kuma tabbatar da doka da oda.