Hamas ta yi zazzafar suka ga gwamnatin Amurka bayan da ta ƙi amincewa da kudurin bangaren tsaro na Majalisar Dinkin Duniya (UNSC) da ke buƙatar tsagaita wuta nan take kuma na dindindin a Zirin Gaza. Hamas ta bayyana wannan mataki a matsayin wani sabbin alamomin nuna son kai da makauniyar goyon baya ga Isra’ila da Amurka ke nunawa.
A wata sanarwa da ta fitar, ƙungiyar ta ce:
“Muna Allah wadarai da wannan mataki na ƙin amincewa da muradun duniya baki ɗaya, kasancewar ƙasashe 14 cikin 15 na kwamitin sun goyi bayan kudurin. Wannan matsayin girman kai na Amurka yana nuna rashin girmama doka ta Ƙasa da Ƙasa da kuma ƙin karɓar kowane yunkuri na dakatar da zubar da jinin ‘yan Falasɗinu.”
Hamas ta ƙara da cewa wannan veto na Amurka ya bai wa Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, "wata dama" don ya ci gaba da “yaƙi da hallaka jama’a da basu ji ba, basu gani ba.”
Ƙungiyar ta kuma yi suka kan raunin da Majalisar Dinkin Duniya ke nunawa wajen ceto Gaza da samar da agaji, tana mai cewa hakan na ta da tambayoyi sosai game da rawar da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa ke takawa, da kuma ingancin dokoki da ƙa’idodin da suka kamata su kare rayukan al’umma.