Alkali Usman, na Babbar Kotun Shari’a ta Birnin Tudu, Karamar Hukumar Gummi, Jihar Zamfara, ya yi nasarar tserewa daga hannun wasu ‘yan bindiga da suka yi garkuwa da shi.
Rahotanni sun nuna cewa Alkali Usman, wanda bayanai suka nuna cewa an sace shi a ranar 26 ga Yuni, ya koma gida lafiya a safiyar Juma’a, 27 ga Yuni, misalin karfe 10 na safe, a cewar wata majiya daga yankin.
Bayan dawowarsa, an garzaya da alkalin asibiti mafi kusa inda ya ke samun kulawar likitoci sannan daga bisani aka sallame shi.
Jami’an tsaro suN yi masa tambayoyi kafin sake hadashi da iyalansa.
Hukumomi ba su bayyana yadda ya yi nasarar tserewa daga hannun masu garkuwa da mutanen ba har zuwa wannan lokaci.
Tags:
Labarai