Majalisar Dattawan Najeriya ta tabbatar da shirin daukar karin matasa 30,000 cikin rundunar ‘yan sandan kasar nan.
Sanata Madori ya bayyana cewa an bai wa Hukumar Kula da Ayyukan ‘Yan Sanda (PSC) izinin daukar karin jami’ai domin cike gibin da ake da su a bangaren.
Ya ce gwamnatin tarayya ta amince da daukar karin matasa 30,000 a wannan shekarar domin inganta tsaro da kuma rage gibi a bangaren ma’aikata.
A cewarsa, “Shugaba Bola Ahmed Tinubu ya bai wa hukumar damar ci gaba da daukar sabbin jami’ai kowace shekara har sai an cike gibi da ake da shi a rundunar.”
Sanatan ya kuma shawarci jama’a da su lura kada su fada hannun 'yan damfara, inda ya ce za a sanar da yadda za a yi daukar aikin ta kafafen yada labarai na kasa.
Tags:
Labarai