Babban sifeton ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bai wa iyalan jami’an ‘yan sanda 13 da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aikin tsaro tallafin kudi fiye da naira miliyan takwas (N8m) a Jihar Anambra.
Tags:
Labarai
Babban sifeton ‘Yan Sanda, Kayode Egbetokun, ya bai wa iyalan jami’an ‘yan sanda 13 da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aikin tsaro tallafin kudi fiye da naira miliyan takwas (N8m) a Jihar Anambra.
Mai magana da yawun ‘yan sanda a jihar, Tochukwu Ikenga, shi ne ya bayyana hakan ta cikin wata sanarwa da ya fitar a daren Juma’a.
Ikenga, wanda Superintendent ne na ‘yan sanda, ya ce Kwamishinan ‘Yan Sanda na Jihar Anambra, Ikioye Orutugu, ne ya mika takardun kudin ga iyalan a madadin Babban Sufeton.
Ya ce Orutugu ya gabatar da wannan tallafin ne a safiyar Juma’a yayin taron wata-wata na jami’ai a dakin taro na shelkwatar rundunar ‘yan sanda ta jihar.
Mai magana da yawun ya kara da cewa cikin wadanda suka amfana har da iyalan wani inspekta da aka harbe shi “ba da gangan ba” da wasu jami’ai rundunar sukayi a shingen binciken tsaro da ke kan hanyar Onacha zuwa Owerri.
Kakakin ya ce, Irin wannan tallafi wani tsari ne da Babban Sufeton ya bullo da shi domin tallafa wa iyalan jami’an da suka rasa rayukansu yayin gudanar da aiki.
Ya kara da cewa, ana sa ran wannan tsari zai kara wa jami’an karsashi da kwarin gwiwa wajen gudanar da ayyukansu cikin kwarewa da jajircewa, tare da tabbatar musu cewa, jin dadin su na daga cikin manyan abubuwan da rundunar ke bai wa muhimmanci.
Ya kuma bayyana cewa wannan shiri yana karkashin tsarin Group Life Assurance da IGP Family Welfare Scheme.