Kungiyar kare hakkin dan Adam ta Amnesty International ta bukaci Gwamnatin tarayya da ta gudanar da cikakken bincike kan kisan gillar da aka yi wa wasu fasinjoji akalla 12 a karamar hukumar Mangu da ke Jihar Filato.
Lamarin, ya faru ne da yammacin ranar Juma’a, yayin da wata motar bas mai kujeru 18, dauke da mutane 31, ke kan hanyar zuwa bikin aure,inda aka kaiwa mutanen cikin ta hari, hakan yayi sanadiyyar mutane 12 suka mutu nan take, yayin da wasu 11 suka jikkata.
A wata sanarwa da Amnesty International ta fitar a ranar Asabar, kungiyar ta jaddada bukatar a tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan danyen aiki sun fuskanci hukuncin gaskiya kuma cikin gaggawa.
Rahotanni sun bayyana cewa bas din mallakin Jami’ar Ahmadu Bello ta Zariya (ABU) na dauke da matafiya daga Basawa, a karamar hukumar Zariya ta Jihar Kaduna, lokacin da aka yi musu kwanton-bauna da misalin karfe 8 na dare a ranar Juma’a. Wasu daga cikin wadanda suka tsira sun tabbatar da cewa mutane 12 ne suka mutu, yayin da sauran suka jikkata sosai.
Wannan kira da Amnesty International ke yi na zuwa ne a daidai lokacin da damuwa ke ƙara ƙaruwa kan yawaitar rikicin ƙabilanci da na addini a yankin.
Ƙungiyar ta yi waiwaye kan makamancin irin wannan mummunan hari da ya faru a watan Agustan 2021, a hanyar Rukuba da ke Jos ta vArewa, inda matafiya 22 da ke dawowa daga bikin Maulidi a Bauchi suka hallaka.
A wata wallafa da kungiyar ta yi a shafinta na X (tsohuwar Twitter), Amnesty International ta ce:
"Kisan gilla da aka yi wa matafiya 12 a jihar Filato abin firgici ne kuma akwai bukatar yin binciken gaggawa mai zaman kansa na gaskiya. Dole ne hukumomin Najeriya su tabbatar da adalci ga wadanda abin ya shafa kuma su hana maimaituwar irin wannan kisan. Watsi da aikata laifuka na kara habaka tashin hankali. #PlateauKillings #JusticeForTravelers.”
Kungiyar ta bukaci gwamnatin Najeriya dakada ta furta kalaman Allah-wadai kawai, ta dauki matakan da suka dace don dakile afkuwar irin wannan ibtila’i a gaba.
Amnesty International ta bayyana kai hare-hare kan matafiya a matsayin babban laifi da ba za a aminta da shi ba, wanda ke nuna rashin darajta rayuwar bil’adama da kin bin doka.
Haka kuma, ta jaddada cewa ya kamata a ba wa wadanda suka jikkata cikakken kulawa ta likitanci domin ceto rayukansu.