Hatsarin Mota Ya Yi Sanadiyyar Mutuwar Mutane a Hanyar Katsina–Dutsinma

Wani mummunan hatsarin mota da ya faru a ranar Asabar kan babban titin Katsina zuwa Dutsinma,  ya yi sanadiyyar mutuwar daukacin Mutanen da ke cikin wata motar da ta kama da wuta.



Lamarin ya shafi wata mota kirar Toyota Camry, mallakin wani mutum, wadda ta sami matsalar birki, ta juya sau da dama, kafin daga bisani ta kama da wuta.

Rahotanni sun ce duka Mutanen da ke cikin motar sun makale suka gagara fitowa har suka kone ba a  ko iya  gane gawar su. Har yanzu ba a tabbatar da adadin su ba a hukumance.

Hukumomin tsaro da jami’an lafiya sun isa wurin domin gudanar da bincike da ceto gawarwakin, yayin da ake ci gaba da kokarin gano asalin wadanda suka rasa rayukansu.

Lamarin ya haifar da dimuwa da alhini a tsakanin al’umma, musamman ma dangane da yadda wuta ta hana ceto rayukan mutanen.

Previous Post Next Post