Ministan harkokin wajen Kasar Saudiyya, Yarima Faisal bin Farhan, ya sake jaddada goyon bayan da Masarautar Saudiyya ke bayarwa ba ga al’ummar Falasɗinu, a yayin bude taro karo na 51 na Majalisar Ministocin Harkokin Wajen Ƙungiyar Ƙasashen Musulmi (OIC) da aka gudanar a Istanbul, Turkiyya, a ranar Asabar.
Yarima Faisal ya kuma yi Allah wadai da hare-haren Isra’ila kan Iran, yana mai bayyana su a matsayin “Abinda bai dace ba” ga dokokin kasa da kasa da kuma keta hurumin Iran da tsaronta.
Taron na Istanbul, wanda Turkiyya ta karɓi bakuncinsa, kuma wa’adin ta na farko a shugabancin na Majalisar Ministocin Harkokin Wajen na OIC. Yarima Faisal ya taya Turkiyya murna bisa karbar shugabancin, tare da godewa Kamaru bisa rawar da ta taka a lokacin da ta ke jagoranci Majalisar a baya.
A jawabinsa, Yarima Faisal ya jaddada muhimmancin da Saudiyya ke baiwa batun Falasɗinu, inda ya bayyana ƙoƙarin da Masarautar ke yi don kawo ƙarshen yaƙin da ake yi a Gaza, da kuma daidaita matsayar ƙasashen larabawa da Musulmi a kan rikicin.
Ya sake nanata cewa Saudiyya na goyon bayan kafa ƙasar Falasɗinu mai cikakken 'yanci bisa iyakar da aka tsara tun 1967 tare da Gabashin Urushalima a matsayin babban birninta.
Dangane da rikicin Isra’ila da Iran, Yarima Faisal ya ce: “Wadannan hare-hare barazana ne ga zaman lafiya da kwanciyar hankali a yankin,” yana mai kira da a dakatar da dukkan ayyukan soja, tare da komawa teburin tattaunawa tsakanin Iran da ƙungiyoyin ƙasa da ƙasa.
Ya kuma bayyana goyon bayan Saudiyya ga ƙoƙarin da ake yi don magance rikicin Yemen, inda ya nuna cikakken goyon baya ga warware rikicin a siyasance da maido da zaman lafiya da tsaro a ƙasar.