Amurka Ta ki Amincewa da Tsagaita Wuta Na Dindindin a Gaza

Bangaren tsaro na Majalisar Dinkin Duniya  (UNSC) ta kada kuri’a kan wani kuduri da ke neman tsagaita wuta na dindindin a Zirin Gaza da saki fursunoni da kuma bada damar shigar da kayayyakin agaji ba tare da tangarɗa ba. Sai dai Amurka ce kaɗai ta ƙi amincewa da kudurin, inda ta yi amfani da karfin kujerar na ƙi ta veto domin hana amincewa da shi.


Wannan ne karo na biyar tun daga watan Oktoban 2023 da Amurka ke hana wucewar kuduri da ya shafi rikicin Gaza a majalisar.


Jakadiyar wucin gadi ta Amurka a MDD, Dorothy Shea, ta bayyana a fili kafin kada kuri’ar cewa Amurka ba za ta goyi bayan kudurin ba. Ta jaddada matsayin Ƙasarta cewa "Isra’ila na da ‘yancin kare kanta," ciki har da kawo ƙarshen Hamas da tabbatar da cewa ba za ta zama barazana ga Isra’ila ba.


Duk da cewa mambobi 14 cikin 15 na kwamitin sun goyi bayan kudurin, Amurka kaɗai ce ta ƙi amincewa da shi, wanda hakan ya dakile wucewar kudurin, duba da matsayin da take da shi a matsayin ɗaya daga cikin mambobin dindindin da ke da ikon veto.


Wannan mataki ya ƙara fito da bambancin ra’ayi da rikici tsakanin kasashe dangane da rikicin Gaza, da kuma ƙara bayyana ƙuncin da al’ummar Gaza ke ciki, sakamakon ci gaba da tashin hankalin da ya dabaibaye yankin.

Previous Post Next Post