Hon. Aliyu Muhammad Tiga, Dan Majalisar Jiha mai wakiltar karamar hukumar Bebejiya rabawa shugabannin al’umma da limamai fiye da mutum 300 manyan riguna da kudin cefanan Sallah a wani bangare na taimakon al’umma.
Wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi sun hada da Hakimai, Dagatai, Masu Unguwanni da Limaman Masallatan Juma’a daga sassa daban-daban na karamar hukumar Bebeji.
“Zan ci gaba da tallafawa Masarautar Bebeji da malamai da limamai a fadin karamar hukumar domin ci gaban su da al’ummarsu,” in ji dan majalisar.
Hakazalika, Hon. Tiga ya bayyana cewa ofishinsa yana da tsare-tsaren ci gaba da tallafa wa matasa ta hanyar daukar nauyin karatunsu. Ya ce tun da farko an dauki nauyin dalibai 70 da za su kammala karatunsu kyauta, kuma shirin zai ci gaba.
A cewar Dan Majalisar “Ina da kudurin ganin matasanmu sun samu ilimi mai nagarta da ya dace da zamani, domin su zama ginshikin ci gaban Bebeji,” .