Hukumar (FDA) da ke kula da ingancin abinci da magunguna ta Amurkata sanar da janye wasu Ƙwayayen kaji daga kasuwa, bayan da aka gano yiwuwar dauke da kwayar cutar Salmonella.
Wannan na zuwa ne bayan mutane 79 sun kamu da cutar, inda 21 daga cikinsu aka kwantar da su a asibiti, kamar yadda hukumar dakile yaduwar cututtuka ta Amurka (CDC) ta tabbatar. Ta ce babu wanda aka ruwaito ya mutu.
Ƙwayayen da aka janye na dauke da sunaye samfura daban-daban, kuma an rarraba su zuwa jihohin Arizona, California, Illinois, Indiana, Nebraska, New Mexico, Nevada, Washington da Wyoming.
Sun shiga hannun manyan shagunan sayar da kayayyaki kamar Walmart, Save Mart, FoodMaxx, Lucky, Smart & Final, Safeway, Raley’s, Food 4 Less da Ralphs.
Cutar Salmonella na daga cikin cututtukan da ke da matukar hadari, musamman ga yara kanana, tsofaffi da masu raunin garkuwar jiki.
Ga masu lafiya kuwa, cutar na iya haddasa zazzabi, gudawa, ciwon ciki, amai da rashin jin dadi gaba daya.
A wata sanarwa da ta fitar, Kamfanin August Egg Company — wanda ya shafe fiye da wata guda da dakatar da sayar da sabbin kwai — ya bayyana cewa: “Tun da muka gano matsalar, mun fara tura dukkan Ƙwayayen zuwa wani kamfani da ke aikin kashe duk wata kwayar cuta kafin a sake dawowa da su kasuwa.”
Hukumar FDA ta shawarci jama’a da su daina amfani da duk wani kwai da abin ya shafa, tare da neman karin bayani daga inda suka siya. Ana kuma shawartar masu sayar da kaya da su cire dukkanin Ƙwan daga shagunan su don kare lafiyar al’umma.