HATSARI A OTAL DIN ‘YAN NAJERIYA A MAKKAH: BA A SAMU ASAR RAI BA

 

Hukumar Hajji ta Kasa (NAHCON) Ta ce gobarar da ta faru a daya daga cikin otal-otal da ke masaukin ‘yan Najeriya a unguwar Shari Mansur, birnin Makkah, a ranar Asabar, ba a rasa rai ba.

Otal ɗin da lamarin ya faru, mai suna Imaratus Sanan, yana dauke da kimanin mahajjata 484 Jirgin yawa (Private Tour Operators).  Ba a samu rasa rai ba, kuma dukkan mahajjatan suna cikin koshin lafiya, tuni ma suka isa Mina cikin aminci.

Gaggawar daukar mataki daga hukumomin bada agajin gaggawa na Saudiyya da ma’aikatan otal ɗin ya taimaka sosai wajen kashe gobarar cikin kankanin lokaci, tare da dakile yaduwar wutar zuwa sauran sassan ginin.


Bayan faruwar lamarin, Shugaban Hukumar NAHCON,
Farfesa Abdullahi Saleh Usman, tare da Kwamishinan Tsare-tsare, Kula da Ma’aikata da Kudi, Alhaji Aliu Abdulrazak, da Mataimakin Kwamishinan Makkah, Daraktan Alidu Shutti, sun kai ziyara wajen domin tantance halin da ake ciki da kuma tabbatar da kula da jin daɗin mahajjatan da abin ya shafa.

Yayin da yake jajanta musu, Farfesa Abdullahi ya bayar da umarnin gaggauta samar da sababbin masauki ga dukkan mahajjatan da lamarin ya shafa. Ya tabbatar musu da cewa hukumar za ta bayar da dukkan taimakon da ya dace domin rage radadin lamarin.

Tuni dai NAHCON ta kammala shirye-shiryen sauya masaukin mahajjatan zuwa wani wuri mai inganci, inda shugaban ya ziyarci sabon ginin da aka tanadar musu domin tabbatar da ingancinsa.

Shugaban na NAHCON da Kwamishinan sun jinjinawa hukumar bada agajin gaggawar da jami’an ta na   Saudiyyabisa kulawar da suka nuna da kuma hadin kai daga ma’aikatan otal ɗin wajen shawo kan lamarin cikin nasara.

Kana ta gode wa Allah Madaukakin Sarki da ya kare rayukan mahajjatan a cikin wannan lamari.

Previous Post Next Post