Mutane 9 Sun Rasa Ransu a Mummunan Hatsarin Mota a Kyaramma, Jihar Jigawa

Wani mummunan hatsarin mota ya faru a garin Kyaramma, karamar hukumar Ringim, Jihar Jigawa, inda motoci biyu kirar Golf 3 suka yi taho-mu-gama.

Motar farko tana kan hanyarta daga Abuja zuwa Gujungu, yayin da ta biyu ke tafiya daga Hadejia zuwa Kano. Hatsarin ya faru ne da misalin karfe 2:00 na daren Asabar,  inda motocin suka kauce daga hanya bayan sun yi karo.

Mutane tara (9) ne suka rasa rayukansu, ciki har da direbobi biyu. Wasu goma sha daya (11) sun jikkata yayin da suke karbar magani a Asibitin Gwamnati na Ringim.

Kwamishinan ‘Yan Sandan Jihar Jigawa, CP AT Abdullahi, ya mika sakon ta’aziyya, ya kuma bukaci direbobi su kiyaye dokokin hanya domin kare rayuka. 

Ana cigaba da bincike kan lamarin.


Previous Post Next Post