Rahotanni daga ƙasar Qatar sun bayyana cewa an ji ƙararrakin fashewar wasu abubuwa masu ƙarfi gaske da ake tunanin bama-bamai ne, yayin da aka ga haske sosai a sararin samaniya a birnin Doha, babban birnin ƙasar.
Lamarin ya faru ne a lokacin da ake kara samu ƙaruwa a fargabar da barazana kan yiwuwar kai hari ga sansanonin sojin Amurka da ke ƙasar.Duk da cewa hukumomin Qatar ko na Amurka ba su fitar da cikakken bayani kan lamarin a hukumance ba, wannan lamari ya jefa al’umma cikin fargaba, musamman ma da yake sansanonin sojin Amurka a yankin sun kasance cikin shirin ko-ta-kwana tun bayan karuwar tashin hankali a yankin Gabas ta Tsakiya.
Za a ci gaba da bibiyar lamarin domin samun karin bayani daga hukumomin tsaro na Amurka da kuma gwamnatin Qatar dangane da asalin abubuwan da suka faru.
Tags:
Labarai