Wasu ’yan bindiga sun hallaka wani makiyayi tare da yin awon gaba da shanunsa da ba a tantance adadinsu ba a karamar hukumar Konduga ta jihar Borno.
Bayanai sun nuna cewa Makiyayin da aka halaka sunana sa Mohammed Audu mai shekaru 31, maharan sun kai masa farmaki ne a lokacin da yake kiwon dabbobinsa.
Ya samu raunin harbin bindiga, inda aka garzaya da shi Asibitin Gwamnati na Jakana, amma likitoci sun tabbatar da rasuwarsa.
Dan uwa ga marigayin, Sanda Audu, ne ya kai rahoton harin ga jami’an tsaro washe gari da safe. Ana zargin maharan sun tsere da shanun zuwa wani wurin da ba a sani ba.
Bayan faruwar harin, sojojin Operation Hadin Kai, ’yan sanda, ’yan sa-kai (CJTF) da maharba sun kai samame yankin. tare da ziyarta wurin da lamarin ya faru, sun tattara shaidu, tare da fara bincike don gano wadanda suka aikata wannan mummunan harin da kuma bibiyar dabbobin da suka sace.
An mika gawar marigayin ga iyalansa domin a yi masa jana’iza kamar yadda addinin Musulunci ya tsara.