Iran Ta Kai Hari Kan Sansanin Sojin Amurka a Qatar Wanda Ya Girgiza Birnin Doha

 A wani babban lamari da ke ƙara tayar da hankali a yankin Gabas ta Tsakiya, ƙasar Iran ta tabbatar da cewa ta kaddamar da hari da makami mai linzami kan sansanin sojin Amurka na Al Udeid da ke birnin Doha, babban birnin ƙasar Qatar.

                                      AI Udeid Air Base Doha 

Rahotanni sun nuna cewa ƙarar fashe-fashe da wani haske a sararin sama sun firgita mazauna Doha da makwabta, musamman bayan Iran ta ayyana wannan farmakin da suna “Annunciation of Victory” – a matsayin ramuwar gayya kan hare-haren da aka kai a kan cibiyoyin nukiliyan ta.

Previous Post Next Post