‘Yan Sanda a Kaduna Sun Fara Bincike Kan Mutuwar Wani Matashi da Aka Zargi JTF da Kashewa

Rundunar ‘Yan sanda a Jihar Kaduna ta bayyana ta Ƙaddamar da bincike kan mutuwar wani matashi mai shekaru 27 da haihuwa, Ibrahim Jibril wanda aka fi sani da “Abba”, wanda ake zargin ‘yan kungiyar tsaro ta JTF sun yi wa dukan kawo wuka har ta kai ga mutuwarsa  a unguwar Matazu da ke yankin Sabon Garin Tudun Wada a Kaduna.



Majiyoyi daga rundunar sun bayyana cewa lamarin ya faru ne  a ranar Lahadi  29 ga Yuni, Babban Limamin Faskari Close, Ibrahim Imam, ya sanar da shugaban al’umma Ibrahim Zuntu cewa jami’an JTF karkashin jagorancin wani Ali wanda aka fi sani da “Commander” sun kama Jibril tare da yi masa duka sosai wanda yayi sanadiyyar mutuwarsa.

Majiyoyin sun ce da misalin karfe 7:00 na safe, bayan samun rahoton, DPO na yankin ya tura tawagar jami'ai zuwa unguwar da lamarin ya faru, inda suka tarar da matashin dauke da munanan raunuka.

“An garzaya da shi asibiti nan take, amma likitan da ya duba shi ya tabbatar da rasuwarsa,” in ji sanarwar.

Daga bisani an mika gawar ga iyalansa don yi masa sutura kamar yadda addinin Musulunci ya tanada,  bayan sun ki amincewa a  binciken  musabbabin mutuwar tasa.

‘Yan sanda sun bayyana cewa duk wadanda ake zargi sun ranta a na kare, amma ana ci gaba da kokarin kama su domin fuskantar hukunci.

Majiyoyin sun kara da cewa binciken da aka fara kan zargin hada baki da kisan kai yana gudana a halin yanzu.

Previous Post Next Post