Ɗan Majalisar Tarayya Ya Nemi Gwamnatin Tarayya Ta Ayyana 1 Ga Muharram A Matsayin Hutu Na Kasa

Ɗan Majalisar Wakilai, Hon. Saidu Musa Abdullahi, da ke wakiltar mazabar Bida/Gbako/Katcha a Jihar Nejaya yi kira ga Gwamnatin Tarayya da ta ayyana ranar ɗaya ga Muharram, wanda ke alamta ranar farkon sabuwar shekarar Musulunci a matsayin hutun kasa.



Abdullahi, wanda shine Mataimakin Shugaban Kwamitin Majalisar kan harkokin kuɗi, ya bayyana hakan ne cikin wata sanarwa da ya fitar a ranar Alhamis.

Ya ce wasu jihohi da dama irin su Neja, Borno, Kano, Katsina, Osun, Oyo da Sokoto na ayyana 1 ga Muharram a matsayin hutu a kowace shekara, don haka ya kamata Gwamnatin Tarayya ma ta bi sahun su.

Ɗan majalisar ya ce “A cikin ƙasa mai tarin al’umma da bambancin addinai kamar Najeriya, girmama ranakun ibada na kowane bangare na taimaka wa wajen ƙarfafa haɗin kai da zaman lafiya,”.

Ya bayyana sabuwar shekarar Musulunci a matsayin lokaci na tunani da sabunta niyya mai kyau, tare da jaddada cewa Hijira na ƙunshe da darussa masu zurfi da suka shafi juriya da sadaukarwa sosai.

Abdullahi ya kuma bukaci ’yan Najeriya da su yi amfani da wannan lokaci wajen yin addu’a domin zaman lafiya, nuna jin ƙai ga juna, da kuma jajircewa wajen cigaban ƙasar.

Previous Post Next Post