WHO Ta Kai Kayan Kula Da Lafiya Na Farko Zuwa Gaza Tun Watan Maris

Hukumar lafiya ta duniya (WHO)  a ranar Alhamis ta bayyana cewa ta samu nasarar kai kayan agajin lafiya  Zirin Gaza a karo na farko tun ranar 2 ga Maris, duk da cewa ta ce kayan da aka kai “ba su taka kara sun karya ba” idan aka kwatanta da bukatun da ake da su a yankin.



Shugaban WHO, Dr. Tedros Adhanom Ghebreyesus, ya bayyana a shafinsa na X cewa kayan da suka hada da jini da plasma da kuma kayayyakin asibiti, za a raba su tsakanin asibitocin Gaza a cikin kwanaki masu zuwa.

Tun ranar 2 ga Maris ne Isra’ila ta ƙaƙabawa Gaza  takunkumi, wanda ya hana ko da kai abinci da magunguna shiga yankin. Sai bayan fiye da watanni biyu ne Isra’ila ta fara bari a shigar da abinci kaɗan, amma sauran kayan agaji sai yanzu aka fara shigarwa.

Dr. Tedros ya ce motocin agaji tara ne suka shiga yankin ta hanyar  mashigar Kerem Shalom da ke tsakanin Isra’ila da Gaza, dauke da kayan asibiti masu matukar muhimmanci, jini guda 2,000 da kuma plasma 1,500. 

Ya ba a sami wani hari ko sace kayan a kan hanyarsu ba, duk da hadurran da ke tattare da tafiyar.

Dr. Tedros ya ce “Wannan dai wani mataki ne mai muhimmanci, amma abu ne da bai kai ya kawo ba,  idan aka yi duba girman bukatun al’umma a Gaza,” i.

Previous Post Next Post