Jami’an Sa-kai Sun Kashe Ƴan Bindiga Uku a Maru, Jihar Zamfara

Aƙalla wasu da ake zargin ƴan bindiga ne guda uku sun mutu a hannun ƴan sa-kai a kauyen Garagi da ke  gundumar Mayanchi a karamar hukumar Maru ta jihar Zamfara.


Rahotanni sun bayyana cewa lamarin ya faru ne da misalin ƙarfe 1:30 na  ranar Laraba, lokacin da ƴan sa-kai suka fafata da ƴan bindigar, inda suka yi nasarar halaka su.

Wannan samame na daga cikin ire-iren matakan tsaro da aka ɗauka na ƙara sanya idanu domin dakile ayyukan ta’addanci da suka addabi yankin.

Ana ci gaba da bincike domin gano asalin waɗanda aka kashe tare da tantance ko suna da alaƙa da wasu gungun masu aikata laifuka da ke kai hare-hare a sassan yankin.

Previous Post Next Post