Netanyahu Na Amfani Yaki Da Iran Domin Ci Gaba da Zama Kan Karagar Mulki

Tsohon Shugaban Ƙasar Amurka, Bill Clinton, ya zargi Firayim Ministan Isra’ila, Benjamin Netanyahu, da yin amfani da yakin Iran domin ya ci gaba da riƙe madafun iko har abada.



Clinton ya bayyana haka ne yayin wata ganawa da ya yi a shirin “The Daily Show,” inda ya ce:
“Netanyahu tun da dadewa yana son yaki da Iran domin hakan zai ba shi damar zama a ofis har abada.”

Tsohon shugaban ya ce na yi kira ga Shugaban Amurka Donald Trump da ya shiga tsakani wajen kawo karshen rikicin da ke tsakanin Isra’ila da Iran, tare da dakile kashe fararen hula da ba su ji-ba basu gani ba.

“Ina ganin kamata ya yi mu yi ƙoƙarin shawo kan wannan rikici. Ina fatan Shugaba Trump zai iya yin hakan,” in ji Clinton.

Sai dai ya bayyana cewa ba ya tunanin  Netanyahu ko Trump na da sha’awar jefa yankin  Gabas ta Tsakiya cikin halin tashin hankali, duk da cewa akwai bukatar Amurka ta ci gaba da kare abokanta a yankin.

Clinton ya jaddada cewa “Muna buƙatar tabbatar wa abokanmu a Gabas ta Tsakiya cewa muna tare da su kuma za mu kare su,”.

Sai dai ya yi suka mai ƙarfi kan salon da wasu kasashen ke bi wajen sanya fararen hula cikin rikici ba tare da an ayyana yaki ba.


A halin yanzu, Amurka ba ta shiga kai tsaye cikin rikicin Iran da Isra’ila ba, sai dai tana ba da taimako ga Isra’ila ta hanyar harbo makamai da suka fito daga Tehran da kuma samar da kayan aikin soji.

Previous Post Next Post