Yawan wadanda aka kama dangane da harin da aka kai a kauyen Yelwata da ke karamar hukumar Guma ta jihar Benue ya karu zuwa 23, bayan da rundunar Intelligence Response Team (IRT) ta kama karin mutane 15.
Rahotonni sun bayyana cewa an kama mutanen ne a ranar Asabar, 22 ga Yuni, a wani bangare na ci gaba da ayyukan tsaro da shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu, ya bayar da umarnin gudanarwa domin kamo wadanda suka aikata wannan mummunan kisan gillar.
A kalla mutane sama da 100 aka kashe lokacin da wasu mahara dauke da makamai suka mamaye Yelwata, harin da yana daga cikin munanan hare-haren da aka taba fuskanta a wannan yankin a shekarar nan.
Wadanda aka kama sun hada da:
Abdulsalam Mohammed, Dahiru Mohammed, Bako Jibril, Abubakar Isa, Abubakar Adamu, Umar Lawali, Bello Tukur, Musa Mohammed, Muazu Idris, Usman Suleman, Dauda Umar, Safiyanu Sani, Isa Yusufa, Babangida Usman, da Yakubu Mamman.
Dukkan su na fuskantar binciken a halin yanzu.
Rundunonin tsaro da suka hada da sojoji, ’yan sanda, da sauran hukumomin tsaro na ci gaba da gudanar da Sintirin hadin-gwiwar da ayyukan tabbatar da tsaro a kauyen Yelwata da makwabtan sa domin hana afkuwar karin rikici da kuma tabbatar da cewa wadanda suka aikata wannan ta’asa sun fuskanci hukunci.
Wani babban jami’in tsaro da ya tabbatar da kama mutanen ya ce bincike na ci gaba da gudana, kuma akwai yuwuwar kama karin mutane a kwanaki masu zuwa.